Dirar Mikiya: Duk wani dan iska ya kuka-da-kan sa - Inji Hafsan sojin saman Najeriya

Dirar Mikiya: Duk wani dan iska ya kuka-da-kan sa - Inji Hafsan sojin saman Najeriya

Hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana a cikin gaggausar murya cewa duk wani hatsabibi da dan iska ya kuka da kan sa domin kuwa jami'an sa sun kara shiri fiye da da don ganin sun ga bayan su cikin kankanin lokaci.

Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da yakai wata ziyarar aiki tare da duba yadda ayyukan jami'an sa dake yaki da 'yan ta'addan dazukan jihar Zamfara dake gudana a halin yanzu a sansanin su na filin sauka da tashin jiragen tunawa da Marigayi Ummaru Musa 'Yar'adua a Katsina.

Dirar Mikiya: Duk wani dan iska ya kuka-da-kan sa - Inji Hafsan sojin saman Najeriya

Dirar Mikiya: Duk wani dan iska ya kuka-da-kan sa - Inji Hafsan sojin saman Najeriya
Source: Facebook

KU KARANTA: Jerin sunayen mutane 24 da za suyi wa APC takarar gwamnoni

Legit.ng Hausa ta samu cewa Air Marshal Sadique Abubakar ya yaba da yadda yakin ke tafiya sannan kuma ya bayyana cewa ayyukan na jami'an sa na rundunar 'Dirar Mikiya' za su fadada ne ya zuwa garuruwan Birnin Gwari da kuma jihar Katsina domin murkushe ta'addancin.

A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta soma sakin sunayen wadanda za suyi takarar kujerun gwamnoni a jahohin Najeriya ashirin da hudu da za'a gudanar da zabukan shekarar 2019.

Haka zalika mun samu cewa hukumar zaben har ila yau ta soma fitar da sunayen wadanda za suyi takarar kujerun 'yan majalisun jahohin tarayyar Najeriya dukkan su da za'a gudanar da zabukan su a shekarar ta 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel