Shehu Sani: An kirkiro Sure-P, N Power don cimma bukatun siyasa ba don cigaban talaka ba

Shehu Sani: An kirkiro Sure-P, N Power don cimma bukatun siyasa ba don cigaban talaka ba

- Shehu Sani, ya ce shirin bayar da tallafi na SURE-P da kuma na NSIP, an kirkiro su ne don cimma wasu bukatu na siyasa ba wai don tallafawa rayuwar talaka ba

- An kirkiro SURE-P a 2012, lokacin Goodluck Jonathan, ya yin da aka kirkiro NSIP a gwamnatin Muhammadu Buhari, da zummar rage yawan marasa aikin yi a kasar

- Sai dai Sani ya ce SURE-P ne burodin cin hanci da rashawa, yayin da N-Power ya zama kamar botar shafawa burodin don yaudarar talaka

Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, ya ce shirin bayar da tallafi na SURE-P da kuma na NSIP, an kirkiro su ne don cimma wasu bukatu na siyasa ba wai don tallafawa rayuwar talaka kacokan ba.

An kirkiro shirin bayar da tallafi na SURE-P a shekarar 2012, lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yin da aka kirkiro shirin bayar da tallafi na NSIP a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da zummar rage yawan marasa aikin yi a kasar.

Sani, ya yi zargin cewa gaba daya shirye shiryen an kirkire su don don zama kamar wata kugiya ta mallake ra'ayoyi da 'yancin talakan Nigeria, da kuma ganin sun ci gaba da goyon bayan gwamnati da jam'iyya mai ci a lokacin.

KARANTA WANNAN: Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2

Shehu Sani: An kirkiro Sure-P, N Power don cimma bukatun siyasa ba don cigaban talaka ba
Shehu Sani: An kirkiro Sure-P, N Power don cimma bukatun siyasa ba don cigaban talaka ba
Asali: Twitter

A cewarsa, jam'iyyar PDP ce ta samar da shirin SURE-P don ci gaba da samun goyon bayan talakawa akan bukatun siyasarta, yayin da ita kuma jam'iyyar APC ta bullo da nata shirin na N-Power don cimma nata manufofin siyasar.

"Dalilin kawai da ya sa aka samar da wadannan shirye shirye na SURE-P da NSIP ba zai wuce samar da hanyoyin mallake zuciyar talaka, ta hanyar yaudararsa da wadannan shirye-shirye, da nufin cimma wasu manufofi na siyasa, amma ba wai an samar da shirye shiryen bane kacokan don ci gaban talaka,' a cewar sa.

Shehu sani ya kara cewa cewa shirin SURE-P da na N-Power duk kugiyoyi ne na sagale 'yanci da soyayyar talaka, don mallake su ta yadda duk inda aka ce su yi, za su yi can ba tare da tambayar dalili ba. An samar da SURE-P kamar burodin cin hanci da rashawa, yayin da N-Power ya zama kamar botar shafawa burodin don yaudarar talaka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel