Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje

Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje

Shuwagabannin kungiyar Izala reshen jahar Kano sun kai ziyara ga gwamnan jahar Kano a fadar gwamnati jahar, inda suka jadda masa goyon bayansu ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, musamman a yayin da yake tunkarar zaben shekarar 2019.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban Malaman Izala, Abdullahi Saleh Pakistan ne ya jagoranci tawagar Malaman zuwa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Rikicin kudin haraji: Kamfanin MTN ta maka gwamnatin tarayya gaban Kotu

Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje
Malam Saleh Pakistan da Ganduje
Asali: Facebook

A yayin wannan ziyarar da suka kai masa, Malaman sun jaddada goyon bayansu a gareshi, sa’annan suka jinjina ma gwamnan bisa muhimman ayyukan da yake yi a jahar Kano, da ma ayyukan da yake yi ga addinin Musulunci.

Idan za’a tuna gwamnan jahar Kano ne babban hadimin addinin Musulunci a jahar Kano watau ‘Khadimul Islama’, wanda ko a satin daya gabata sai da gwamnan ya musuluntar da maguzawa da sama da dari biyu.

Sai dai jama’a da dama sun nuna rashin jin dadinsu da wannan ziyara, musamman a wannan lokacin da ake zargin gwamnan da karbar cin hanci da rashawa da suka kai dala miliyan biyar daga hannun wasu yan kwangiloli.

Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje
Malaman da Ganduje
Asali: Facebook

Masu irin wannan ra’ayi na ganin Malaman sun nuna goyon bayanzu ga gwamnan a fili, wanda a cewarsu kamata ya yi Malamai su kasance masu daidaita sahun al’umma ba wai su dinga goyon bayan masu mulki akan rashin gaskiya ba.

A wani labarin kuma, dan kwangilar daya baiwa Ganduje makudan kudaden nan har ma ya daukeshi wannan bidiyon ya bayyana ma majalisar dokokin jahar Kano cewa zai gurfana gabansu amma fa sai Gwamna Ganduje da shugaban Hisbah Aminu Daurawa sun halarci zaman.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel