Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2

Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2

- Shugaban majalisar dattijai ta kasa, Bukola Saraki, ya bukaci mambobin majalisar da su tabbata sun amince da sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da makwanni 2

- Saraki ya ce sabuwar dokar wacce idan aka tabbatar da ita, za ta magance dukkanin matsalolin da ake fuskanta a cikin ayyukan rundunar 'yan sandan kasar

- Legit.ng Hausa, ta tattara maku bayanai, kan wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani dangane da wannan sabuwar doka

Shugaban majalisar dattijai ta kasa, Bukola Saraki, ya bukaci mambobin majalisar da su tabbata sun amince da sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da makwanni 2, wanda a cewarsa, tuntuni ne ya kamata ace majalisar ta amince da dokar don samun damar sauraron ra'ayoyin jama'a.

Saraki ya ce sabuwar dokar wacce idan aka tabbatar da ita, za ta magance dukkanin matsalolin da ake fuskanta a cikin ayyukan rundunar 'yan sandan kasar.

KARANTA WANNAN: Sabon rahoto: Yan Nigeria Miliyan 2 ne ka karbar maganin cutar HIV - NACA

Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2

Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2
Source: Depositphotos

Wannan kuwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, matarsa Nwanneka Ekweremadu da kuma yaronsa suka tsallake rijiya ta baya baya a ranar Talata, bayan da aka kai masu hari a gidansa da ke rukunin gidaje na Apo, a babban birnin tarayya Abuja.

ABUBUWA 10 GAME DA SABUWAR DOKAR SAKE FASALIN RUNUNDUNAR YAN SANDA

1. Sanata Bala Na'Allah, daga mazabar Kebbi ta Kudu ne ya gabatar da wannan kudirin doka

2. Dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, zai samar da sabon tsari na yadda za a dai-daita ayyukan rundunar ya koma gogayya da na manyan kasashen duniya

3. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, zai samar da wani muhimmin tsari da zai tabbatar da kare 'yanci da martabar kowanne dan Nigeria

4. Dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, za ta samar da wani tsari na tabbatar da ganowa tare da dakile ta'addanci, cafke masu laifi da kuma gurfanar da su don yi masu hukunci ba tare da bata lokaci ba, ta hanyar amfani da duk wasu dokoki da take da iko akansu.

5. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, za ta tabbatar an samar da wani kyakkyawan yanayi na hadin guiwa da taimakekeniya tsakanin rundunar 'yan sanda da jama'ar gari.

6. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, zai canjawa rundunar suna daga "Nigerian Police Force" zuwa "Nigerian Police".

7. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, ta HARAMTAWA jami'in dan sandan da yake kula da wanda ake zargi, zuwa kotu a matsayin jami'i mai shigar da kara, don tabbatar da yin adalci da gaskiya a wajen shari'ar wanda ake zargin.

8. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, ta bukaci sake fasalin matakan bayar da belin mutanen da aka cafkesu ba tare da takardar waranti ba. A cewar sabuwar dokar, bai kamata a tsare irin wadannan mutane har sama da awanni 24 ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

9. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, ta HARAMTAWA jami'an 'yan sanda shan giya ko wasu nau'in kayan maye a lokacin da suke bakin aiki; haka zalika ta samar da wata hukuma ta musamman don karbar korafe korafen jama'a akan jami'an rundunar.

10. Sabuwar dokar sake fasalin rundunar 'yan sandan, ta kuma dora alhakkin duk wani abu da zai biyo baya sakamakon tsare mai laifi ba bisa ka'ida ba, ko kuma bincike da cafke wanda ake zargi ba bisa ka'ida ba, akan jami'in da ya aikata hakan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel