Boko Haram sun kashe soja daya, wasu 16 sun bace

Boko Haram sun kashe soja daya, wasu 16 sun bace

Labari da muke samu ya nuna cewa Boko Haram sun kai wa sojojin Kasa-da-kasa na Najeriya hare-hare a ranakun 5 da 6 ga watan Nuwamba, sannan kuma sun hallaka soja daya, 16 kuma sun bace ba a san inda suke ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hakan ya kasance ne a harin da suka kai wa sojoji a sansanin kauyen Kukawa a ranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba, da kuma wata nakiya da ta tashi da wata motar sojoji a Mallam Fatori ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba.

Dukkan wadannan kauyuka su na Arewacin Borno ne kuma su na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Boko Haram sun yi kokarin ganin sun yi galaba a wani shingen bincike da sojoji suka kafa a ranar Litinin, wanda Sojojin Musamman na 101 da kuma na Bataliya ta 157 ne ke wurin.

Sun kai harin ne wajen 5:40 na yamma.

Boko Haram sun kashe soja daya, wasu 16 sun bace
Boko Haram sun kashe soja daya, wasu 16 sun bace
Asali: Depositphotos

Premium Times ta kuma bayyana cewa sun fatattaki sojojin kuma suka kona motocin daukar sojoji biyu, sannan suka gudu da zabgegiyar bindigar kakkabo jiragen yaki guda daya.

Majiyar ta ce daga nan sai Boko Haram suka karasa cikin gine-ginen wata sakandare da aka kaurace ba a karatu a cikin ta, amma sojoji ke amfani da gine-ginen a matsayin sansanin su. Sun kone dakin gudanarwar sansanin kuma suka kone dakin dafuwar abinci da duk abin da ke cikin sa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Buhari ba abin yarda ba ne – Atiku

A wannan farmakin ne suka kashe soja daya, 16 kuma suka bace, ba a san inda suke ba, har zuwa Laraba da dare babu labarin su.

Sai dai kuma Boko Haram sun tsere yayin da suka ga sojojin sama a cikin helikwafta sun kai dauki.

An rika bin su da helikwafta ana kai musu hari, amma suka tsere suka koma cikin mabuyar su.

Majiya ta ce sojojin sama na can na tantance irin barnar da aka yi, domin mika rahoto a hedikwatar sojoji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel