Wasan taka leda: An dawo cigaba da buga gasar cin kofin zakarun Turai

Wasan taka leda: An dawo cigaba da buga gasar cin kofin zakarun Turai

Rahotanni sun bayyana cewa a yau (Alhamis) ne aka cigaba da fafatawa a wasannin taka leda na cin kofin zakarun nahiyar Turai (Europa League), na matakin rukuni, na 2018/19. A gasar cin kofun, kungiyoyin kwallon kafa 4i ne da suka fito daga kasashen Turai za su fafata a wasanni 24 na gasar.

Da misalin karfe 4 da minti 50 ne na yammacin yau, agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi, aka fara buga wasan, tsakanin Fanerbach ta kasar Turkiya da Anderlecht da ke Belgium, sai kuma inda Astana ke kan fafatawa da Jablonec a halin yanzu.

Da misalin karfe shida da minti hamsin da biyar kuwa za'a buga wasannin ne kamar haka, Akhisarspor da Sevilla, FK Krasnodar da Standard Liege, FC Astana zasu kece raini da FK Jablonec, Dynamo Kiev, da Rennes.

KARANTA WANNAN: Nigeria ce ta 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a - Buhari

Wasan taka leda: An dawo cigaba da buga gasar cin kofin zakarun Turai
Wasan taka leda: An dawo cigaba da buga gasar cin kofin zakarun Turai
Asali: Getty Images

BATE Borisov kuwa zata karbi bakuncin Chelsea sai MOL Vidi da PAOK Salonika, Lazio da Olympicos Marseilles, Spartak Moscow, da Rangers, Gent da Basekktas, Apollon Limassol, da Frankfurt na kasar Jamus, Malmo na kasar Sweden da Sparsborg.

Da misalin karfe 9:00pm, kungiyar kwallon kafa ta Celtic za ta fafata da RB Leipzig na kasar jamus, Real Betis da AC Milan, Arsenal a kasar Ingila zasu karbi bakuncin Sporting dake kasar Portugal, sai Girondis da Zenit, Bayern Leverkusen da Zurich, Vorskla Poltava da FK Qarabag.

Sauran wasannin kuwa sun hada da Dinamo Zagreb da Spartak Trnava, sai Olympiakos da F91 Dudelange, Slavia Prague FC da Copenhagen.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng