Saboda N50,000, matashi ya kashe mahaifiyarsa, ya kwanta da gawarta
Hukumar yan sandan jihar Edo ta damke wani matashi dan shekara 18 mai suna, Samuel Akpobome Emobor, wanda ya hallaka mahaifiyarsa sannan yayi lalata da gawarta domin asirin kudi.
Wani boka mai sayar da kwaya a unguwar ne ya tuntsura wannan matashi aikata wannan aika-aika.
Samuel ya bayyana cewa bokan yayi masa alkawarin kudi dubu hamsin idan ya kashe mahaifiyarsa kuma ya kwanta da gawarta.
Ya ce sau daya kacal ya kwanta da mahaifiyarsa kuma ya kasheta ne yayinda take bacci.
KU KARANTA: APC ta roki jigo a jam'iyyar da kar ya canja sheka
“Na so yin amfani da mahaifiyata domin asiri. Shekaru na 18. Mahaifina ya mutu. Wani mutum mai suna ‘One Love’ ne ya fada min inyi amfani da mahaifiyata domin asirin kudi. Ya yi alkawarin bani N50,000 idan na kasheta kuma na kwanta da ita."
“Ya ce in cire kunnenta da yan yatsunta in kai masa. Ina gab da ciresu kenan mutane suka shigo.”
“Na makure mahaifiyata ne yayinda take barci. ‘One love’ kwaya yake sayarwa. Ya sa min wani abu cikin abin sha sannan ya fada min inje in kashe mahaifiyata.”
“Ranan da na kai yan sanda gidansa, ya gudu. Ni dan garin Oghara ne, a kamfanin ruwa nike aiki.”
“Yanzu ina nadama saboda mutane sun min dukan tsiya.”
Kwamishanan yan sandan jihar, Babatunde Kokumo, ya ce za’a gurfanar da shi a kotu ba da dadewa ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng