‘Yan bindiga sun kashe wani hamshakin mai kudi a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe wani hamshakin mai kudi a Katsina

Labarin da ke zuwa mana sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum, Alhaji Nasiru Maimasara, a kwatas din Gachi da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.

An tattaro cewa ‘yan bindiga sun sace ‘yar mutumin a yayin da ta ke yunkurin guduwa daga inda lamarin ya afku.

Rahoton ya nuna cewa abun ya faru ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba.

‘Yan bindiga sun kashe wani hamshakin mai kudi a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe wani hamshakin mai kudi a Katsina
Source: Depositphotos

A yayin da wani mutum wanda ya shaida faruwar lamari ya ke jawabi ga manema labarai ya ce: “ 'yan bindigan sun kai mamaya yankin sannan suka fara harbe a yayin da suka nufi gidan Alhajin da suka kashe a kwatas din Gachi.

“‘Yan bindigan sun kashe Alhajin ne a yayin da ya ke yunkurin tserewa daga nan suka sace ‘yarsa.

“Bayan ‘yan bindigan sun tafi aka yi hanzari aka garzaya da Alhajin babban asibitin Kankia inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An samu hargitsi a majalisa kan manufofin gwamnatin Buhari

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina, Mista Gambo Isa ya tabbatat da faruwar hakan.

Isa ya ce rundunar tana iya kokarinta wajen cafke ‘yan bindigan da suka aikata wannan mummunar aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel