Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

Wani dan majalisar wakilai a zauren majalisar taraya dake wakiltar mazabar Taura da Ringim a jihar Jigawa dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Muhammad Gausu Boyi ya sha da kyar a hannun wasu mafusatan matasa.

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, lamarin dai ya faru ne a garin Dutse dake zaman babban birnin jihar inda dan majalisar tare da wasu magoya bayan sa suka je domin tantance su a gabanin zabukan fitar da gwani da za'a gudanar.

Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa
Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An fitar da alkaluman yan shi'ar da aka kashe tun bayan hawan Buhari mulki

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai isar sa farfajiyar tantancewar sai ya gamu da matasa inda suka yi masa ihu tare da fadan kalaman batanci gare shi har ma suka so su buge shi.

A wani labarin kuma, Kungiyar masana kimiyyar ruwa a Najeriya watau Association of Hydrologists in Nigeria a turance sun yi karin haske game da yiwuwar afkuwar girgizar kasa a kasar Najeriya musamman ma a garin Abuja da jahohin da ke makwaftaka da ita.

Shugaban kungiyar na kasa Farfesa Ehidiamhen Charles Olumese ya shaidawa 'yan jarida a yayin wani babban taron da kungiyar ke yi a garin Minna, jihar Neja cewa ko kusa abu ne mai matukar wuya samun girgizar kasar a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng