An fitar da alkaluman yawan 'yan shi'ar da aka kashe tun bayan hawan Buhari mulki

An fitar da alkaluman yawan 'yan shi'ar da aka kashe tun bayan hawan Buhari mulki

Babban kwararren lauyan kasa da kasa kuma mai rajin kare hakkin bil'adama Mista Femi Falana ya aike da takardar koke zuwa ga hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya watau National Human Rights Commission a turance yana bukatar ta kaddamar da bincike kan kisan da ya kira na gilla akan 'yan shi'a a Najeriya.

Haka zalika Lauyan wanda ya ce akalla tun da Shugaba Buhari ya hau mulki jami'an tsaron Najeriya sun kashe 'yan shi'ar 492, ya kuma yi barazanar shigar da kara kotun duniya idan har hukumar bata yi yadda ya bukata ba.

An fitar da alkaluman yawan 'yan shi'ar da aka kashe tun bayan hawan Buhari mulki
An fitar da alkaluman yawan 'yan shi'ar da aka kashe tun bayan hawan Buhari mulki
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta samu cewa 'yan shi'ar almajiran Zakzaky sun yi artabu da jami'an tsaron Najeriya a lokunta da kuma wurare da dama a cigaba da zanga-zangar ganin an saki shugaban su da ake cigaba da tsarewa.

A wani labarin kuma, Wasu manyan bankuna na kasa da kasa watau HSBC da kuma UBS sun tattara komatsan su sun fice daga Najeriya biyo bayan dalilan da ake kyautata zaton na da nasaba da tabarbarewar tattalin arzikin kasar da Najeriya ke fuskanta.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani daftarin rahoto da babban bankin Najeriya watau CBN ya fitar a ranar Juma'ar da ta gabata inda yake bayanin dalilan da yasa kudaden kasar waje suka yi karanci a kasar ta Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng