Shari'ar Dino Melaye ta gamu da tangarda a gaban alkalin kotu a Abuja

Shari'ar Dino Melaye ta gamu da tangarda a gaban alkalin kotu a Abuja

Shari'ar da Sanata Dino Melaye, Sanatan dake wakiltar mazabar jihar Kogi ta gabas dake a gaban alkalin wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayya a unguwar Maitama ta gamu da sabuwar tangarda.

Mun samu cewa alkalin kotun dai ya katse zaman sauraron shari'ar ne a dai dai lokacin da daya daga cikin shaidun masu kara yake bayar da sheda akan tuhumar da ake yi wa Sanatan saboda rashin bin doka wajen gabatar da shi.

Shari'ar Dino Melaye ta gamu da tangarda a gaban alkalin kotu a Abuja
Shari'ar Dino Melaye ta gamu da tangarda a gaban alkalin kotu a Abuja
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi wani sabon nadi mai muhimmaci

Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko lauyan wanda ke kare kan sa watau Sanata Dino Melaye shine ya ankarar da alkalin rashin bin ka'idar da lauyoyin masu karar suka yi wajen gabatar da shaidar su gaban kotun.

Daga nan ne sai alkalin ya dage cigaba da sauraron shari'ar har sai dukkan bangarorin sun shirya tsaf sannan a cigaba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Sanata Dino Melaye yana fuskantar tuhuma ne bisa zargin karya da kuma bayar da bayanan da ba gaskiya ba akan Shugaban Ma'aikatan Gwamnan jihar kogi na cewa ya kitsa kisan sa a watannin baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng