Tattalin arziki: Bayan dakatarwa, Najeriya zata cigaba da fitar da ganyen Zobo kasar Mexico

Tattalin arziki: Bayan dakatarwa, Najeriya zata cigaba da fitar da ganyen Zobo kasar Mexico

Hukumar ajiyan amfanin gona ta Najeriya wato Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS) ta bayyana cewa Najeriya zata cigaba da fitar da ganyen Zobo kasar Mexico, a nahiyar Amurka ta kudu.

Diraktan hukumar, Dr Vincent Isegbe, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai NAN a yau Talata, 6 ga watan Nuwamba a birnin tarayya Abuja.

Ya ce a shekarar 2017, Najeriya ta fitar da kwantena 1,983 na Zobo zuwa kasar Mexico kadai, kuma an samu kudi $35 miliyan cikin watanni tara kacal.

Ya kara da cewa an dakatar da fitarwan ne sakamakon wani kwaro da ya addabi ganyen yayin ajiya a Najeriya.

KU KARANTA: Kotu ta ba Orji Kalu kwanaki 7 ya gurfana a gaban ta

Yace: “Yanzu mun shawo kan al’amarin, shi yasa zamu cigaba da fitar da ganyen. Nan da makonni kadan zamu fitar.”

“Manomanmu sun kosa kuma an shirya komai. Za’a fara girban Zobon nan ba da dadewa ba.”

“Kuma abin farin cikin shine, Najeriya na da kyan yabanya, ana girba a dukkan lokutan shekara.”

“Ya kamata muyi amfani da wannan dama domin samarwa kasarmu kudin canji da kuma taimakawa gwamnatin nan wajen fadada tattalin arzikin Najeriya.”

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana niyyar fadada tattalin arzikin kasar domin rage dogaro da arzikin man fetur. Hakan ya zama wajibi ne bisa ga fadin farashin danyen mn fetur wanda ya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki a shekarar 2016.

Hakan yasa aka fara tunanin karfafa fannin aikin noma a fadin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng