Sam babu adalci: Yadda sojoji, 'yan sanda suka kashe 'yan Shi'a 492 - Falana
- Mr. Femi Falana (SAN), ya kalubalanci hukumar NHRC, da ta soma bincike kan yadda jami'an soji dana 'yan sanda suka kashe mabiya akidar Shi'a har 492 tun daga 2014 zuwa yanzu
- A takardar kalubalen da kai koke da ya rubuta mai kwanan wata, 2, ga watan Nuwamba, 2018, Falana ya baiwa hukumar wa'adin kwanaki bakwai ta gudanar da wannan bincike
- Akalla 'yan Shi'a 49 ne aka kashe a arangamarsu da jami'an tsaro a Abuja, a zanga zanga da suka gudanar don a saki shugabansu Sheik Ibraheem El-Zakzaky da ke tsare tun 2015
Babban lauyan nan da ke fafutukar kare hakkin Bil-Adama, Mr. Femi Falana (SAN), ya kalubalanci hukumar kiyaye hakkokin dan Adam ta kasa, inda ya bukace ta da ta soma bincike kan yadda jami'an soji dana 'yan sanda suka kashe mabiya akidar Shi'a har 492 tun daga 2014 zuwa yanzu.
A takardar kalubalen da kai koke da ya rubuta mai kwanan wata, 2, ga watan Nuwamba, 2018, zuwa ga babban sakataren hukumar ta NHRC, Mr. Anthony Ojukwu, Falana ya baiwa hukumar wa'adin kwanaki bakwai ta gudanar da wannan bincike.
Mr. Femi Falana, ya yi barazanar cewa ma damar hukumar NHRC ta gaza cimma wannan bukata tasa kafin cikar wa'adin, to kuwa zai tabbata ya tattara rahoto kan abun da ya kira 'nuna wariya ga mabiya wata akida da kuma ta'addanci ga dan Adam; wanda jami'an tsaron gwamnatin tarayya suka aikata, kana ya aikawa kotun sauraron kararrakin ta'addanci ta kasa da kasa, kamar yadda yake kunshe a cikin bayani na 7 a kundin dokokin kasar Roma.
KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kungiyar kwadago ta janye shiga yajin aiki, gwamnati za ta biya N30,000

Asali: Depositphotos
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan wasikar ta sa, ta isa shelkwatar hukumar a ranar Litinin, inda a ciki ya bayyana cewa: "Domin tabbatar da cewa an dakile jami'an tsaron gwamnatin tarayya wadanda su 'yan Sunna ne daga kashe rayuka 'yan Shi'a, cikin gaggawa na bukaci hukumarku ta tabbata ta kawo karshen cin zarafin da akeyiwa 'yan Shi'a ba tare da bata lokaci ba.
"Tun da dai har gwamnatin tarayya ta kasa ayyana mabiya akidar Shi'a a matsayin kungiyar 'yan ta'adda kamar yadda ta ayyana kungiyar Boko Haram a baya, to ya zama wajibi hukumar kiyaye hakkin bil Adama ta kasa ta soma bincike kan irin kiran gillar da aka yiwa 'yan shi'ar," a cewar Falana.
KARANTA WANNAN: Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa
Wasikar ta ci gaba da cewa, "Ku sani cewa, idan kuka gaza cika wannan bukata tawa a cikin wa'adin kwanaki bakwai da na deba maku, to kuwa babu makawa, zan rubuta rahoto kan 'nuna wariya ga mabiya wata akida da kuma ta'addanci ga dan Adam; wanda jami'an tsaron gwamnatin tarayya suka aikata, kana ya aikawa kotun sauraron kararrakin ta'addanci ta kasa da kasa, kamar yadda yake kunshe a cikin bayani na 7 a kundin dokokin kasar Roma."
Akalla 'yan Shi'a 49 ne aka kashe a arangamarsu da jami'an tsaro a Abuja, a wata zanga zanga da suka gudanar idan suka bukaci a saki shugabansu Sheik Ibraheem Yakub El-Zakzaky, da matarsa, wadanda gwamnatin tarayya ke tsare da su tun a shekarar 2015.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng