Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Kano ya sauya sheka daga PDP zuwa PRP
Shugaban marasa rinjaye a majalisa kuma mamba mai wakiltan yankin Kura/Garun Malam a majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Abdullahi Muhammad-Chiromawa ya sauya sheka daa jam’iyyar PDP zuwa PRP.
Dan majalisan ya sanar da sauya shekarsa yayinda yake zantawa da manema labarai aranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba a jihar Kano.
Muhammad-Chiromawa ya kuma sanar da cewar ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar.

Asali: Depositphotos
A cewarsa ya yanke shawarar barin PDP zuwa PRP domin bin sahun ubangidansa a harkar siyasa wato Alhaji Salihu Sagir-Takai, wanda ya koma PRP a kwanan nan.
Ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar ne saboda saba dokar da suka yiwa manyan jam’iyyun siyasa biyu katutu a jihar.
KU KARANTA KUMA: Atiku zai je kasar Amurka a karshen Nuwamba - Okupe
Ku tuna cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar wanda yayi murabus daga matsayinsa zuwa PDP ya sake sauya sheka zuwa PRP a kwanan nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng