Munafunci dodo: An zargi wasu gwamnonin APC 3 da shirya wa Buhari gadar zare
Shugaban wata kungiya dake rajin kare muradun gwamnatin shugaba Buhari da kuma fafutukar ganin ya lashe zaben shekarar 2019 watau Federation of Buhari Support Group, mai suna Ibrahim Sikiru yace sun gano wasu gwamnonin APC 3 da ba su son Buhari.
Ibrahim Sikiru, wanda ya ce gwamnonin da ke yi wa kan su lakani da masu ra'ayin 'yan mazan jiya, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ke jagorantar makarkashiyar cin dunduniyar shugaba Buhari din.

Asali: Facebook
KU KARANTA: An cafke asurgimin kwarto a Kano
Legit.ng Hausa ta samu cewa sauran gwamnonin da kungiyar ta zarga da yi wa shugaban kasar zagon kasa sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Gwamna Ahmad Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, da kuma Gwamna Jubrilla Bindow na jihar Adamawa.
A wani labarin kuma, Wasu manyan bankuna na kasa da kasa watau HSBC da kuma UBS sun tattara komatsan su sun fice daga Najeriya biyo bayan dalilan da ake kyautata zaton na da nasaba da tabarbarewar tattalin arzikin kasar da Najeriya ke fuskanta.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani daftarin rahoto da babban bankin Najeriya watau CBN ya fitar a ranar Juma'ar da ta gabata inda yake bayanin dalilan da yasa kudaden kasar waje suka yi karanci a kasar ta Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng