Sun takulo tsuliyar dodo: Sojojin Najeriya 149 na shan gwale-gwale saboda anfani da soshiyal midiya
Akalla jami'iyan sojin Najeriya 149 ne yanzu haka ke fuskantar hukunci bisa samun su da laifin da hukumar rundunar su ta sojoji ta yi na anfani da soshiyal midiya ba bisa ka'ida ba a karo na farko tun bayan kafa masu sharuda da dokokin yin hakan.
Majiyar mu ta Premium Times ta samu cewa jami'an rundunar da aka samu da laifin dai yawancin su duk kananan sojoji ne kuma sun fito daga bangaren sojin kasa, na sama da ma na ruwa.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Lauyan Sule Lamido ya koma APC
Legit.ng Hausa ta samu cewa dokar ta anfani da soshiyal midiya a gidan sojan ta fara aiki ne tun a watan Yulin da ya gabata kuma dokar tayi kakkausan hani ga dora hotuna cikin kakin soji da kuma sauran muhimman wuraren aikin su ga sojojin.
Haka zalika majiyar ta mu ta samu tabbacin cewa ana kan hukunta masu laifin ne daga bakin babban daraktan hukumar rundunar sojin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng