Ka daina raba kudin Najeriya kamar wani goro - Atiku ya caccaki Buhari a kan kyautar kudi

Ka daina raba kudin Najeriya kamar wani goro - Atiku ya caccaki Buhari a kan kyautar kudi

- Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarci shugaba Buhari ya zama mai taka tsan-tsan da dukiyar kasa

- A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya bawa kasar ta Guinea Bissau kyautar $500,000 gabanin zaben da kasar za ta yi a ranar 18 watan Nuwamba

- Sai dai a wani jawabi da Atiku ya fitar a yau, Lahadi, ya ce arzikin Najeriya kamata ya yi ya amfani 'yan Najeriya tare da zargin gwamnatin Buhari da yin almubazzaranci da dukiyar kasa

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, ya shawarci Buhari a kan ya zama mai taka tsan-tsan da dukiyar kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na wannan kalamai ne a matsayin raddi ga shugaba Buhari bayan ya bawa kasar Guinea Bissau.

A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya bawa kasar ta Guinea Bissau kyautar $500,000 gabanin zaben da kasar za ta yi a ranar 18 watan Nuwamba.

Ka daina raba kudin Najeriya kamar wani goro - Atiku ya caccaki Buhari a kan kyautar kudi
Atiku da Buhari
Asali: Twitter

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ne ya sanar da hakan yayin da ya karbi bakuncin wakilin majalisar dinkin duniya a kasar Guinea Bissau a Abuja, ranar Talata.

DUBA WANNAN: Rage farashin man fetur: Ku yi hankali da Atiku - Jigo a APC

Onyeama ya bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta bawa kasar ta Guinea gudunmawar kayan aiki da motoci domin kasar ta samu sukunin yin zabe cikin nasara.

Sai dai a wani jawabi da Atiku ya fitar a yau, Lahadi, ya ce arzikin Najeriya kamata ya yi ya amfani 'yan Najeriya tare da zargin gwamnatin Buhari da yin almubazzaranci da dukiyar kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng