Arewa gida: Za'a bude wani katafaren kamfanin sarrafa tumatur a wata jihar Arewa
Wani hamshakin dan kasuwa kuma mai kishin kasa, Alhaji Muhammadu Usman Sarki ya kammala gina wani katafaren kamfanin Sarrafa tumatur din gwangwani a jihar Katsina dake a Arewa maso yammacin Najeriya da ya sanyawa suna Aldusar.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa kamfanin dai za'a bude shi sannan kuma ya soma aikin gadan-gadan nan ba da dadewa inda ake sa ran dubun dubatar al'umma tun daga manoma zuwa ma'aikata za su samu aikin yi.

Asali: Original
KU KARANTA: Za mu ba kowa dama a zabi ra'ayin sa a 2019 - Buhari
Legit.ng Hausa ta samu cewa jihar ta Katsina dai na cikin jahohin da ake noman tumatur da yawan gaske amma kuma saboda rashin masana'antu da kamfuna da za su sarrafa shi yakan lalace ba tare an anfanu da shi ba.
A wani labarin kuma an samu sabani tare da musayar yawu a tsakanin hukumar nan dake da alhakin shiryawa tare da gabatar da jarabawar kammala Sakandare ta kasashen yammacin Afrika watau West African Examinations Council (WAEC) da kuma shugaba Buhari game da sakamakon jarawabar sa.
Yayin da hukumar ta WAEC ta dage akan lallai shugaban kasar, Muhammadu Buhari shi ne ya rubuta tare da neman hukumar da ta gabatar masa da sakamakon sa na jarabarar kammala Sakandare, daga fadar shugaban kasar su kuma sun ce hukumar ce don kashin kanta taga damar yin hakan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng