Yadda wata mace ta halaka kanta bayan kashe mijinta da yaransu uku

Yadda wata mace ta halaka kanta bayan kashe mijinta da yaransu uku

Mutanen unguwar Vandeikya da ke Makurdi a jihar Benue sun shiga bakin ciki da juyayi bayan wata mace ta kashe kanta bayan halaka mijinta da yaransu guda uku.

Rahotanni sun bayyana cewar mijin matar mai suna Nicholas Adetsav ma'aikaci a karamar hukumar Makurdi yayin da matarsa itama ma'aikaciyar gwamnati ne.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Moses Yamu ya shaidawa kamfanin dillanin labarai NAN cewar ana kyautata zaton matar ne ta kashe mijin da kuma yaran.

Yadda wata mace ta halaka kanta bayan kashe mijinta da yaransu uku
Yadda wata mace ta halaka kanta bayan kashe mijinta da yaransu uku
Asali: Facebook

"Munyi imanin cewar matar ne ta kashe sauran iyalan sannan ta kashe kanta," inji Yamu.

DUBA WANNAN: Ban karba ko kwandala ba daga hannun 'yan kwangila - Ganduje

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewar makwabta sun tabbatar musu da cewar matar tana yawan fada da mijinta duk da cewa babu wanda ya san abinda ke haifar ra rikicin.

Ya ce jami'in dan sanda da aka aika ya gudanar da bincike a gidan ya tsinci gawar mijin ta kumfa a bakinsa, sai kuma gawar yaransu uku da gawar matar rike da wuka a hannunta.

Makwabta sunce ce sun hangi matar da dauke da tabarya za ta ragargaji motar mijinta a ranar Juma'a amma babu wanda ya tanka musu domin matar da gargadi makwabtan su dena yin katsalandan cikin lamarin gidan ta.

Yamu ya ce tuni 'yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano abinda ya janyo mutuwar iyalin yayin da an ajiye gawarsu a asibitin St. Theresa da ke Makurdi.

Kafin rasuwarsu, mijin yana aiki ne da sashin kudi yayin da matar na aiki da sashin aikin gona na karamar hukumar Makurdi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164