Fasahar matasa: Wani matashi ya kirkiri injin dake maida tarkacen ledoji zuwa fetur a Najeriya (Hotuna)
Wani matashi a Najeriya mai tarin fasaha mai suna Emeka Nelson ya samu fikirar kera wani injin mai ban mamakin gaske da zai taimakawa muhalli da kuma inganta rayuwar 'yan Najeriya idan har aka kara bashi kwarin gwuiwa.
Matashin dai Emeka yace injin din da ya kera yana markadewa tare da tace tarkacen bola kamar su ledoji da kuma robobi inda kuma yake sarrafa su ya zuwa man fetur domin anfanin al'umma.

Asali: Facebook

Asali: UGC

Asali: Facebook
Legit.ng Hausa ta samu cewa matashin dai ya saka hotunan injin din ne a shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Facebook wanda har yanzu yana cigaba da jan hankalin al'ummar kasar musamman ma matasa.

Asali: Facebook
Haka zalika matashin ya kara da cewa da fasahar kirkirerren injin din tasa wadda ya sawa suna Mgbanwe C12 zai iya mayar da tarkacen na bola ya ziwa man gas na manyan motoci da kalanzir dama kwanon rufin gidaje ko buloluwan zamani.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng