Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)

Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)

Babban da namiji a halin yanzu na shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari watau Yusuf Buhari ya soma shirin nan na dole ga dukkan matasa a Najeriya da suka kamma karatun digirin su watau National Youth Service Corps (NYSC).

Kamar dai yadda muka samu, hotunan Yusuf din sanye da kakin 'yan NYSC din dai sun soma yawo tun jiya a dandalin sadarwar zamani inda kuma muka samu cewa a sansanin yiwa kasa hidima na Kubuwa ne ya soma.

Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)
Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)
Asali: Instagram

Legit.ng Hausa dai ta tuna cewa a watan Disemba din shekarar bara ne Yusuf ya samu mummunan hatsarin babur a cikin garin Abuja wanda ya jaza masa mummunan ciwukan da har sai da ya kwanta asibi.

Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)
Dole-uwar-naki: Yusuf Buhari ma ya fara shirin bautar kasa (Hotuna)
Asali: Instagram

KU KARANTA: Sauya sheka: An kunyata Kwankwaso a jihar Kebbi

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da tsafta da kuma sahihancin abinci da magungunan 'yan Najeriya watau National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC) a turance ta gargadi 'yan Najeriya da cin wani samfurin kifi da tace yana da guba.

Shugabar hukumar ta National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye ce dai ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun ta daga hedikwatar hukumar dake a garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng