Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya

Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da tsafta da kuma sahihancin abinci da magungunan 'yan Najeriya watau National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC) a turance ta gargadi 'yan Najeriya da cin wani samfurin kifi da tace yana da guba.

Shugabar hukumar ta National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye ce dai ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun ta daga hedikwatar hukumar dake a garin Abuja.

Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya
Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta samu cewa kifin da hukumar ta bankado mai guba din dai sunan sa Puffer Fish kuma yanzu haka ya shiga lungu da sakon kasar nan a don haka ne ma suke bayar da gargadin.

Daga karshe kuma ta shawarci mutane da masu shagunan sayar da abinci da su kula yayin da ita ma hukumar zata sa ido don ganin an yi wa tufkar hanci.

Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya
Hattara jama'a: Hukumar NAFDAC ta bankado wani kifi mai guba a kasuwannin Najeriya
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, Wasu kungiyoyin fararen hula da kuma wasu kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba sun bukaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya harmta addini ko akidar shi'a gaba daya a Najeriya.

Haka zalika kungiyoyin wadanda suka kira taron manema labarai a garin Abuja, sun kuma yi kakkausan kashedi ga 'yan siyasda game da siyasantar da harkar tsaron kasar nan musamman ma ganin cewa zabukan 2019 na ta kara karatowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng