Badakalar $5m: AFRICMIL ta bukaci EFCC, ICPC su soma bincike kan bidiyon Ganduje
- AFRICMIL, ta bukaci hukumomin EFCC da ICPC, da su soma binciken faya fayen bidiyon da ke nuna , Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci daga hannun 'yan kwangila
- A cewar AFRICMIL, babu wani waje a cikin sashe na 308 na kundintsarin mulkin kasar da ya hana EFCC da ICPC gudanar da bincike kan Mr. Ganduje, musamman idan akan rashawa ne
- AFRICMIL ta jinjinawa jaridar Daily Nigeria bisa bankado wannan badakala, da kuma jinjinawa namijin kokarin wanda ya samu damar nade bidiyon
Cibiyar da ke fafutukar bayar da ilimin kafofin sadarwa da tattarawa tare da watsa labarai ta Afrika, AFRICMIL, ta bukaci hukumar EFCC da kuma hukuma mai zaman kanta da ke yaki don dakile cin hanci da rashawa da sauran dangoginsu ICPC, da su soma binciken faya fayen bidiyon da aka wallafa, da ke nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci daga hannun 'yan kwangila
A cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja a ranar Alhamis, kodinetan AFRICMIL, Chido Onumah, ya bayyana wannan zargi da ake wa gwamnan da kuma faya fayen bidiyon da aka fitar a matsayin "lamarin da yafi karfin a yi kurum"
"Zargin na da karfi. Dukkanin faya fayen bidiyon da muka gani na ci gaba da bayyana wani boyayyen al'amari kan zargin, kuma hakan ya sa lamarin ya fi karfin a zura idanuwa ana kallo kawai," cewar Onumah.
KARANTA WANNAN: Amaechi: Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019

Asali: Twitter
Ya bukaci hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa da su tashi tsaye don yin bincike kan wannan zargi, da kuma tattara bayanai don hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin badakalar.
"Mun lura cewa kamar hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa sun ja sun yi shiru akan wannan zargin, watakil ko don saboda garkuwar da dokar kasa ta baiwa Mr. Ganduje. Duk da haka, ba wai shiru ne za su yi ba, domin dokar ba ta hana su gudanar da bincike kan lamarin ba," a cewar sa.
A cewar Onumah, babu wani waje a cikin sashe na 308 na kundintsarin mulkin kasar da ya baiwa shugaban kasa ko gwamnoni kariya, wanda kuma ya hana hukumomin yaki da cin hanci da rashawa gudanar da bincike kan Mr. Ganduje, musamman idan akan tuhuma ne.
"Don haka ya zama wajibi ICPC da EFCC su gudanar da kwakkwaran bincike kan wadannan faya fayen bidiyo wanda a yanzu ya zama kamar cin fuska ga kasar. Haka zalika ya kamata hukumomin su fara shirin hukunta Mr. Ganduje da zaran an same shi dumu dumu da aikata laifin," a cewar Onumah.
Ya kuma jinjinawa jaridar yanar gizo ta Daily Nigeria bisa bankado wannan badakala, da kuma jinjinawa namijin kokarin wanda ya samu damar nade bidiyon don kwarmaton cin hanci da rashawa.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Wannan zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng