Amaechi: Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019

Amaechi: Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019

- Rotimi Amaechi, ya ce shugaban kasar zai amince da sakamakon zaben 2019, walau shi ne ya samu nasara ko akasin haka

- Amaechi ya ce jam'iyya mai mulki ta APC, za ta kasance mai bin dokokin da ke tattare da zabe na kasar sau da kafa a babban zabe mai zuwa

- Tun farko, Ketil Karlsen, jagoran tawagar ta EU a Nigeria da kuma ECOWAS, ya ce kungiyar EU za ta yi hadin guiwa da Nigeria don gudanar da sahihin zabe a 2029

Rotimi Amaechi, babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, ya ce shugaban kasar zai amince da sakamakon zaben 2019, walau shi ne ya samu nasara ko akasin haka.

Da ya ke jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga kungiyar hadakar kasashen turai (EU), Amaechi ya ce jam'iyya mai mulki ta APC, za ta kasance mai bin dokokin da ke tattare da zabe na kasar sau da kafa a babban zabe mai zuwa.

Ya baiwa tawagar tabbacin cewa: "Zamu tsaya bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, kuma zamu amince da duk wani hukunci da ta yanke. Muna da yakinin cewa, kamar yadda muka yiwa yan Nigeria alkawarin samun canji, to kuwa ku da kanku za ku fahimci canjin da muke nufin samarwa.

KARANTA WANNAN: Aisha Buhari: Sai da gwamnatin Buhari ta zo 'yan Nigeria suke shan romon demokaradiyya

Amaechi: Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019
Amaechi: Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019
Asali: Depositphotos

Ya ce a lokacin zaben 2015, lokacin yana matsayin gwamna, gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta cire masa duk wasu jami'an tsaro tare da fuskantar hare hare ba adadi, sai dai ya ce a mulkin Buhari ba haka take ba, babu gwamnan da aka cirewa jami'an tsaro ko kai masa farmaki saboda yana a wata jam'iyyar hamayya.

Tun farko, Ketil Karlsen, jagoran tawagar ta EU a Nigeria da kuma ECOWAS, ya ce kungiyar EU za ta yi hadin guiwa da Nigeria don gudanar da sahihin zabe a 2029. Ya yi nuni da cewa, EU ta damu matuka na ganin cewa Nigeria ta samu tsarin zabe mai inganci da ya zarce na kowa.

"Mun kashe sama da Euro Miliyan 100 don tallafawa shirye shiryen zaben. A yanzu haka, muna goyonbayan hukumar INEC, muna goyon bayan majalisun tarayya, muna goyon bayan demokaradiyyar hamayya a siyasa kuma muna goyon bayan dukkanin masu ruwa da tsaki," a cewae Mr. Ketil.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Wannan zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng