'Yan Kwankwasiyya 5,000 sun koma jam'iyyar APC a wannan jihar ta Arewa
Kimanin mutane dubu biyar ne masoya tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi'u Musa kwankwaso suka sauya sheka ya zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Kebbi.
Shi dai Sanata Kwankwaso yanzu haka babban jigo ne a jam'iyyar PDP tun bayan da ya fice daga jam'iyyar APC kuma har ma ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta PDP amma bai samu nasara ba.

Asali: UGC
Legit.ng Hausa ta samu cewa magoya bayan Sanatan daga kungiyoyi da dama sun samu kyakkyawar tarba ne a hannun mataimakin gwamnan jihar Alhaji Samaila Yombe a Sakatariyar jam'iyyar ta APC a garin Birnin Kebbi.
Haka zalika da yake jawabi a madadin dukkan wadanda suka koma APC din, tsohon Sakataren tsare-tsare na tafiyar Kwankwasiya a jihar Abdullahi Nayalwa ya ce kyawawan manufofin gwamnatin Shugaba Buhari da Gwamna Atiku Bagudu ne suka sa su sauya shekar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng