Abdullahi Ganduje: Mun bunkasa rayuwar matasa 200,000 a cikin shekaru ukku

Abdullahi Ganduje: Mun bunkasa rayuwar matasa 200,000 a cikin shekaru ukku

- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta bunkasa rayuwar akalla matasa 200,000 tun bayan da aka rantsar da shi akan karagar gwamnan jihar

- Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da irin wannan kokari da nufin bunkasa rayuwar jama'a don ci gaban jihar dama kasar baki daya

- Gwamnan ya kara da cewa irin namijin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da hakan, wanda ya haifar da samawa akalla matasa 50,000 aiki a fadin jihar

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta bunkasa rayuwar akalla matasa 200,000 a cikin jihar tun bayan da aka rantsar da shi akan karagar gwamnan jihar, kusan shekaru uku da rabi a yanzu.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da irin wannan kokari da nufin bunkasa rayuwar jama'a don ci gaban jihar dama kasar baki daya.

Ganduje ya bayyana hakan ne a wani bukin kaddamar da shirin bunkasa rayuwar mutane 4,400 da kuma bude shirin horaswa na kwanaki biyu don kanana da matsakaitun yan kasuwa a fannin noma, karkashin shirin gwamnatin jihar na AGSMEIS, a babban dakin wasa a Sani Abacha da ke Kofar Mata, cikin Kano.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Yar aikin gida ta sace tare da tserewa da kayan N500,000 mallakin matar gidan

Abdullahi Ganduje: Mun bunkasa rayuwar matasa 200,000 a cikin shekaru ukku
Abdullahi Ganduje: Mun bunkasa rayuwar matasa 200,000 a cikin shekaru ukku
Asali: Twitter

A bukin bayar da tallafin a kuma bude shirin horaswar, gwamnan ya ce "Mun shirya bunkasa rayuwar masu yin tallace tallace a bakin titi da suka kai 4,400, da kuma bude shirin horaswa ga mutane akalla 45,000 don amfana da shirin bayar da tallafi ga kanana da matsakaitun yan kasuwa a fannin noma, wanda zamu fara horas da mutane 5,000 a kashi na farko na shirin."

Domin tariyo yadda gwamnatinsa ta fara bunkasa matasa a jihar, Ganduje ya ce: "Kamar yadda kuka sani, daga hawan wannan gwamnati zuwa yau, mun tashi tsaye haikan don yaki da rashin aikin yi a tsakanin matasan jihar, kuma don haka, muka bullo da shirye shirye da dama wadanda zasu kawo karshen wadannan matsaloli."

Gwamnan ya kara da cewa irin namijin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da hakan, wanda ya haifar da samawa akalla matasa 50,000 aiki a fadin jihar, ya kuma ce gwamnatin ta samu damar bunkasa rayuwar wasu matasan ta hanyar horas dasu sarrafa na'urori masu kwakwalwa da dangoginsu da kuma shirin koyar da sana'o'in dogoro da kai.

SANARWA: A kwanan nan ne shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Wannan sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da shafinmu na Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng