Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan PDP ya koma APC a jihar Bauchi
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya sauya sheka daga jam’iyyar Green Party of Nigeria (GNP) zuwa All Progressive Congress (APC) mai mulki a jihar Bauchi.
Tsohon kwamishinan sa kan harkokin addinai a lokacin gwamnatin Yuguda karkashin PDP, Salisu Ahmed Barau ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a jiya Laraba, 3 ga watan Oktoba.
Barau ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan ya koma APC ne domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.
Salisu Barau ya kuma sanar da cewa tsohon gwamnan ya sauya sheka ne tare da magoya bayansa a fadin kasar a karkashin kungiyar Yuguda Alheri.

Asali: Depositphotos
Ya bayyana cewa zuwa yanzu mutane sama da 500,000 sun yi rijistan magoya bayansu inda suka bayar da tabbacin cewa za su samar da kuri’u sama da miliyan guda.
KU KARANTA KUMA: APC na shirin yin sabon bincike a dukiyar Atiku
Ya kuma yi bayanin cewa Yuuda bai bar jam’iyyar GPN saboda wani sabani ba sai dai bayan tattaunawa da ya yi da magoya bayansa a fadin kasar sannan sun kara da cewa wasu magoya bayan nasa da tsoffin hadimansa na wasu jam’iyyun siyasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng