Babbar magana: Yar aikin gida ta sace tare da tserewa da kayan N500,000 mallakin matar gidan

Babbar magana: Yar aikin gida ta sace tare da tserewa da kayan N500,000 mallakin matar gidan

Sau tari, 'yan aikin da aka dauka don tallafawa iyalai aikace aikacen gida, na sanya kawunansu cikin dabi'ar 'yan dauke-dauken kayan mutanen gidan, wanda kuma hakan cin amana ne. Irin wannan lamari ya faru a jihar Legas, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

Queen, mai shekaru 18, na aiki a gidan wata mata da aka bayyana sunanta da Mrs Omowunmi Omojide, wacce rahotonni suka bayyana cewa ta sace kayan mai gidan tare da tserewa da su.

Rahotanni sun bayyana cewa yarinyar ta tsere daga gidana a ranar 19 ga watan Oktoba, bayan da ta samu nasarar sace kayan matar gidan da kudinsu ya kai N500,000.

KARANTA WANNAN: Karin albashi: Gwamnati ba ta yiwa ma'aikata adalci ba - ASUU, SSANU

QUEEN: Yar aikin da ta sacewa uwar gidanta kayan N500,000
QUEEN: Yar aikin da ta sacewa uwar gidanta kayan N500,000
Asali: UGC

Bisa dai yadda ita mai gidan ta shaidawa jaridar Punch, Omowunmi ta ce lokacin da lamarin ya afku, ita ta fita wani bukin taya murnar zagayowar ranar haihuwa, da misalin karfe 8 na dare da ta dawo, sai ta taras da yaranta na garari a cikin gidan su kadai.

Wannan ne ya sa ta fara tunanin ko lafiya ko akasinta. Nan take ta fara neman Queen wacce ya kamata ace tana kula da yaran. Da ta bincika, sai makwafta suka shaida mata cewa 'yar aikin tata ta je siyo wani abu tun wajen karfe 7 na yamma, wanda har zuwa lokacin bata dawo ba.

A binciken da ta yi cikin gidan, nan ne ta gane cewa kayan da ta siyo ta ajiye, babu su babu alamar su, kayan kuwa sun hada da kayan da take sayarwa a shagonta wanda bata dade da yin odar su ba. Bisa rahotanni, Omowunmi na da shagon sayar da kayan sawa, sai dai saboda wasu dalilai ta kwaso kayan ta mayar da su gida.

Bayan wadannan kaya da ake zargin Queen ta sace, ta kuma sace kayan yaran gidan, agoguna da takalman matar gidan.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jiahr Ogun, CHIKE Obi, ya tabbatar da faruwar wannan al'amari inda kuma ya bayyana matakan da rundunar ke bi don gurfanar da Queen akan aikata wannan laifi.

SANARWA: A kwanan nan ne shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Wannan kuwa babban sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da shafinmu na Legit.ng don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng