2019: Manyan malamai 500 sun yi azumi da addu’o’i kan tazarcen Buhari

2019: Manyan malamai 500 sun yi azumi da addu’o’i kan tazarcen Buhari

Yayinda zaben 2019 ke gabatowa akalla sama da malamai 500 da addinai daban-daban ne suka taru a jiya Laraba, 31 ga watan Oktoba a Unity Fountain, Abuja domin ci gaba da addu’o’i kwanaki 40 da azumin da suka shirya domin tabbatar da tazarcen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

Malaman wanda suka hada da na Musulunci, da Kirista sun samu kariya nay an sanda da dama da kuma sauran jami’an tsaro, sun bayyana cewa duk da cewar sun banbanta wajen addini, suna da buri guda na son ganin Buhari yayi nasara.

Baya ga addu’o’i daban-daban daga malaman Musulunci da na Kirista, an kuma gano su suna rungumar junansu domin wanzar da zaman lafiya da hadin kai.

2019: Manyan malamai 500 sun yi azumi da addu’o’i kan tazarcen Buhari
2019: Manyan malamai 500 sun yi azumi da addu’o’i kan tazarcen Buhari
Asali: Facebook

Daya daga cikin manyan fastocin, Bishop Sunday Garba ya bayyana cewa addu’a da azumin da suke yi sun fara ne tun kwanaki 20 da suka gabata kuma za su ci gaba sannan cewa Shugaba Buhari ne zai yi nasara a shekara mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: APC na shirin yin sabon bincike a dukiyar Atiku

Shugaban malaman Musulunci, Imam Kamarudeen Salawu, yace akwai bukatar lura daga dukkanin addinai domin hana baragurbin mutane da suka zo da kudade don siyan zukatansu ko kuma neman addu’ansu.

Ya bukaci Allah ya yi masu zabi na gari ya kuma yaye masu duhu tare da kawo haske.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng