APC na shirin yin sabon bincike a dukiyar Atiku
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa wasu manyan jami’an jam’iyyar APC na kokarin yin amfani da karfinsu a hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na tarayya wajen yin bincike a kadarori na miliyoyin dala da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya mallaka.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kungiyar kamfen din Atiku da suke martani sunce suna maraba da duk irin haka indai har ba zai zamo mayar farauta ba.
Kungiyar kamfen din tace hakan abun mamaki ne cewa bayan sama da shekaru uku, sai yanzu gwamnatin Buhari ta farka domin bincikar tsohon mataimakin shugaban kasar.

Asali: Depositphotos
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Abubakar ya ce ma’aikatarsa c eke dauke da mafi yawan ma’aikata a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter, yayinda yake tattauna bukatar samar da ayyuka a Najeriya.
KU KARANTA KUMA: An yi addu'ar cika shekara 15 da rasuwan Sheikh Ahmadu Yarwa Abulafathi Maiduguri a Karshi Abuja (hotuna)
Ya ce a yanzu haka kamfanoninsa na Najeriya na dauke da ma’aikata 50,000.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng