Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Bayelsa ta fara biyan mata masu juna biyu ihisanin N3,000

Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Bayelsa ta fara biyan mata masu juna biyu ihisanin N3,000

- Gwamnatin jihar Bayelsa ta fara rabawa mata masu dauke da juna biyu ihisanin N3,000 a wani shirinta mai taken 'Safe Motherhood Scheme'

- Gwamna Okowa, wanda ya kaddamar da shirin a matsayin bako na musamman, ya jinjinawa Gwamna Dickson bisa yunkurinsa na gudanar da ayyukan raya al'umar jiharsa

- Gwamna Dickson, a nashi jawabin, ya ce gwamnatinsa ta samar da cibiyoyin kiwon lafiya a gundumomi 105 da ke jihar don magance matsalolin lafiya

Gwamnatin jihar Bayelsa ta fara rabawa mata masu dauke da juna biyu ihisanin N3,000 a wani shirinta mai taken 'Safe Motherhood Scheme', domin bunkasa rayuwar matan da kuma jariran a lokacin goyon cikin da kuma bayan haihuwarsu.

Shirin dai ya jawo yawo da jinjina da kuma tallafi daga wasu jiga jigai a kasar Nigeria, da suka hada da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

Gwamna Okowa, wanda ya kaddamar da shirin da kuma gabatar da rabon kudin ga mata masu dauke da juna biyu da suka ci gajiyar shirin, a matsayin bako na musamman a taron, ya jinjinawa Gwamna Dickson bisa yunkurinsa na gudanar da ayyukan raya al'umar jiharsa, wanda ya kamata ace sauran gwamnoni sun yi koyi da shi.

KARANTA WANNAN: Taka leda: Neymar na iya fuskantar hukuncin zaman wakafi saboda komawarsa Barcelona

Gwamna Dickson tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Gwamna Dickson tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Depositphotos

Gwamna Okowa ya jinjinawa takwaransa na jihar Bayelsa bisa tunawa da matsayin iyaye a cikin al'umma, yana mai jaddada cewa baiwa iyaye mata muhimmiyar kula zai taimaka ainun wajen samar da lafiyayyar al'umma a fadin kasar.

A yayin da ya ke karfafa guiwar iyaye mata wajen amfani da wannan shiri ta yadda ya dace, kamar dai yadda aka samar da shi dominsu, ya shawarce su akan rungumar tsarin bayar da tazarar haihuwa don lafiyarsu da kuma ci gaban iyalansu gaba daya.

Gwamna Dickson, a nashi jawabin, ya ce shirin zai taimakawa yunkurin gwamnatinsa a daukar matakan kawo ci gaba, kamar na shirin inshorar lafiya da kuma samar da cibiyoyin kiwon lafiya, wanda aka samar a gundumomi 105 da ke jihar don magance matsalolin lafiya da al'umomin ka iya fuskanta.

A nashi bangaren, Alhaji Turaki, wanda ya taba neman takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya yi nuni da cewa, bayan samar da gine gine, Gwamna Dickson ya kuma nuna soyayyarsa ga jama'arsa musamman ta hanyar bullo da wannan shirin na "Safe Mothermood Scheme".

A na shi jawabin, kwamishin lafiya, Farfesa Ebitimitula Etebu, ya yabawa gwamnan bisa daukar wannan namiji aiki na bullo da shirye shiryen kiwon lafiya da nufin bunkasa rayuwar al'umar jihar.

SANARWA: A kwanan nan ne shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Wannan kuwa babban sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da shafinmu na Legit.ng don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng