Yadda na sulale na fice daga Najeriya ta barauniyar hanya sadda aka kaimun samame - Nnamdi Kanu
Hatsabibi Nnamdi Kanu dake zaman jagorar wata harmatattar kungiya dake fafutukar ganin tabbatuwar rabuwar kasar Najeriya tare da kafa sabuwar kasar Biafra watau Indigenous People of Biafra, IPOB a turance ya bayyana yadda ya sulale ya fice daga kasar Najeriya ta batauniyar hanya a watannin baya.
Nnamdi Kanu dai ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da gidan Talabijin na kasar Israila inda yace wasu ne suka yi fasa-kwaorin sa suka fita dashi daga kasar Najeriya tare da taimakon 'yan uwan sa.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Buhari ya kai kololuwa na rashin sanin yakamata - Atiku
Legit.ng Hausa ta tsinkaye shi yana cewa: "sanannen lamari ne cewar a watannin baya na koma kasa ta Najeriya inda na cigaba da fafutuka ta da kuma gudanar da addini na na yahudanci, kwatsam sai ga jami'an tsaro da suka zo su dauki raina."
Ya cigaba da cewa amma hakan bata yiwu ba inda wasu daga cikin magoya bayan sa da 'yan uwa suka taimaka masa wajen sulalewa ta barauiyar hanya kafin daga bisani ya yanke shawarar zuwa kasar Isra'ila.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng