Rashin godiyar Allah: Asirin wata hamshakiyar attajirar almajira ya tonu

Rashin godiyar Allah: Asirin wata hamshakiyar attajirar almajira ya tonu

Asirin wata hamshakiyar attajirar almajira mai shekaru 79 a duniya 'yar asalin kasar Chana dake bara a tashar jirgin kasa dake a unguwar Hangzhou ya tonu bayan da wani almajirin da ya santa ya tona ta.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar mu ta Global Times ta ruwaito cewa matar hamshakiyar mai kudi ce da ta fito daga gidan attajira kuma tana da manyan 'ya'ya masu kudi da ke daukar nauyin ta amma ta dage tana bara.

Rashin godiyar Allah: Asirin wata hamshakiyar attajirar almajira ya tonu
Rashin godiyar Allah: Asirin wata hamshakiyar attajirar almajira ya tonu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Manyan makaman da rundunar sojin Najeriya ta siyo sun iso

Legit.ng ta samu cewa da mahukuntan tashar jirgin kasar suka gane ta kuma taki yadda da ta dena barar sai kawai suka rika ankarar da matafiya cewar su dena bata sadakar ko ta roka domin bata da bukata.

Wani dan karamin bincike da aka gudanar akan almajirar dai ya tabbatar da cewa matar ta mallaki kadarori da dama da suka hada da gidajen haya da kuma ababen hawa da dama a garuruwa daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng