Zanga-zangan NLC: Sanata Sani ya yaba ma kungiyar kwadago, ya ce Najeriya na iya biyan N30,000
Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya kaddamar da goyon bayansa ga kungiyar kwadago na Najeriya (NLC).
Sani wanda ya kasance mamba a jam’iyyar Redemption Party (PRP), ya ce zanga-zangar gama gari da kungiyar kwadagon ta shirya abun yabawa ne.
A ranar Talata, 30 ga watan Oktoba ne shugabannin kungiyar NLC a fadin kasar suka fito a jihohinsu daban-daban don wayar wa ýan Najeriya kai kan kudirinsu na Karin albashi.
Shugabannin sun sha alwashin tsayawa akan bakar su na N30,000, inda suka zargi gwamnoni da rashin aminci da kuma karya yarjejeniyar da suka kulla baya.

Source: Depositphotos
Da yake nuna goyon bayansa ga shugabannin kungiyar, Shehu Sani ya ce: “Wadanda za su iya biyan N22,000 a matsayin albashi mafi karanci, su cikasa ladansu kawai su kara N8,000 akai ya zama N30,000. Tattalin arzikin Najeriya zai iya dauka.
KU KARANTA KUMA: Idan ba a maida albashi N30, 000 ba; za a gani a akwatin zabe Inji NLC
“Dole a ci gaba da fafutukar. Zan taya su daga murya a zauren majalisar dattawa.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng
Asali: Legit.ng