Kiwon lafiya: Sabuwar cutar 'Shan Inna' ta bulla Daura da wasu garuruwan jihar Katsina
Rahoton da Legit.ng ke samu daga jihar Katsina, na nuni da cewa, wata sabuwar cutar 'shan Inna' ta bulla a cikin kananan hukumomi guda hudu da ke a cikin jihar. Bullar cutar mai suna 'Type 2 Polio' ta jawo hankalin gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki da ya tursasa su gudanar da zaman gaggawa don dakile yaduwarta.
Da wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin masu tallafawa gwamnatin jihar Katsina ta fuskar kafofin sada zumunta da watsa labarai, Muhammad Barmo, ya tabbatar da bullar sabuwar cutar.
Muhammad Barmo, ya bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar Katsina, QS Alhaji Mannir Yakubu, wanda shi ne shugaban kwamitin rigakafin cutar shan inna a jihar, ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jiya Talata, 30 ga watan Oktoba, 2018 a ofishinsa da ke cikin fadar gwamnatin jihar.
KARANTA WANNAN: Kotu ta dage karar da aka shigar ta bukatar majalisun tarayya su tsige Buhari

Asali: Facebook
Taron gaggawar wanda ya samu halartar likitoci, masu rike da sarautun gargajiya, ya karkata ne kan samar da hanyoyin dakile sabuwar cutar daga yaduwa cikin jama'a da kuma daukar matakin gaggawa na gudanar da rikafin shan inna a fadin jihar.
Mr. Barmo, ya zayyana kananan hukumomin da cutar ta bulla a cikinsu da suka hada da, Zango, Sandamu, Baure da kuma karamar hukumar Daura, yana mai cewa "Sabuwar cutar ta shan Inna, na dauke da dukkanin alamomin da cutar shan inna ke dauke da su, sai dai ita wannan cutar ba ta kai barazanar babbar cutar shan inna ba, amma gwamnati na yin bakin kokarinta na dakile yaduwar cutar."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng