'Yan kabilar Ibo sun sanar da wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar Najeriya

'Yan kabilar Ibo sun sanar da wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar Najeriya

Mataimakin wata kungiyar kiristoci a Najeriya kuma mamba a majalisar koli ta masarautun gargajiyar 'yan kabilar Ibo Eze Dakta Oliver Ohanwe ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya kwantar da hankalin sa game da 'yankin Inyamurai domin kuwa shi za su zaba.

Eze Ohanwe da ke zaman Sarkin masarautar Ihim dake a karamar hukumar Isiala Mbano a cikin jihar Imo ya bayyana cewa su sun riga sun gama yin lissafin su sun gano zabar shugaba Muhammadu Buhari ne kawai zai basu damar samun dan kabilar su ya zama shugaban kasa a 2023.

'Yan kabilar Ibo sun sanar da wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar Najeriya
'Yan kabilar Ibo sun sanar da wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar Najeriya
Asali: UGC

Legit.ng cewa Ohanwe ya bayyana cewa duba da kyawawan manufofin shugaba Buhari da kuma son mulki ya dawo masu a 2023, babu makawa sai sun zabi jam'iyyar ta APC.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) dake zaman Sakataren jam'iyyar a jihar Abia dake yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma yankin 'yan kabilar Ibo mai suna Perfect Okorie yayi wa 'yan uwan sa alkawarin kujerar shugaban majalisar dattawa.

Mista Okorie ya kuma ce a don haka ne ma yake rokon 'yan uwan nasa da su yi wa jam'iyyar ta APC da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ruwan kuri'u a zabukan 2019 da ke tafe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng