Reshe-zai-juye-da-mujiya: Sheidu sun fara fallasa yadda APC ta tafka magudi a zaben jihar Ekiti
Daya daga cikin shaidun masu gabatar da kara a gaban alkalin kotun zabe na zaben da ya gudana na gwamnan jihar Etiki ya bayyanawa kotun cewa daya daga cikin jami'an hukumar zabe ta INEC ya lalata wasu kuri'un jam'iyyar PDP da gangan.
Mai bayar da shaidar, Mista Omobuljo Bankole ya bayyana cewa a rumfar zabe dake wata mazaba ta karamar hukumar Ido-Osi baturen zabe yayi kutun-kutun tare da jami'an jam'iyyar APC wajen yin magudi.

Asali: Original
KU KARANTA: Buhari yace kowa ya zabi wanda ran sa ya kwanta masa
Legit.ng Hausa ta samu cewa jam'iyyar ta PDP dai tare da jagorancin dan takarar ta na gwamnan jihar Ekiti Farfesa Olusola Kolapo sun garzaya kotu suna kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a tsakiyar watan Yulin da ya gabata.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar Abuja, babban birnin tarayya sun sanar da samun nasarar cafke akalla 'yan shi'a almajiran Malam Zakzaky sakamakon artabu da dauki-ba-dadin da suke ta yi da su a ranar Talata.
Kwamishin 'yan sandan Bala Ciroma shine ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda suka kama din ga manema labarai a hedikwatar su dake a garin Abuja.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng