A shirye nake na biya sabon mafi karancin Albashin Ma'aikata - Ortom

A shirye nake na biya sabon mafi karancin Albashin Ma'aikata - Ortom

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya sha alwashin biyan sabon mafi karancin albashin ga ma'aikatansa da gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadago ke shirin amincewa a kasar nan.

Gwamna Ortom ya bayyana hakan ne a yau Talata yayin da wasu mambobin kungiyar kwadago suka ziyarce shi har fada a birnin Makurdi domin bayyana goyon bayan su yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tafkawa muhawara kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyar kwadago ta sha alwashin dirfafar yajin aiki gadan-gadan muddin gwamnatin tarayya ba ta amince da bukatar N30, 000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

A shirye nake na biya sabon mafi karancin Albashin Ma'aikata - Ortom
A shirye nake na biya sabon mafi karancin Albashin Ma'aikata - Ortom
Asali: Depositphotos

Gwamnan jihar Benuwe ya bayyana cewa a shirye yake ya biya ma'aikatan jihar sa dukkanin sabon mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadago suka amince a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Magoya bayan Kwankwaso 5000 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kebbi

A jiya Litinin gwamnatin tarayya ta gudanar da wata muhimmiyar ganawa tare gwamnonin kasar nan domin tuntubarsu kan muhawarar ta da kungiyar kwadago kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito, gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya tarayya da gwamnan jihar Benuwe wajen cirar wannan tuta ta shan alwashin tare da zama cikin shirin biyan duk mafi karancin albashin ma'aikata da gwamnatin tarayya ta amince a kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng