Babbar magana: Wani lauya ya mari DPO tare da yaga masa kaki, ya kuma fasa kan DCO
Da fari dai labarin kamar abun al'amara, ace wai an mari DPO tare da yaga masa kaki, harma takai ga an rotsa kan DCO, duk a lokaci daya. Sai dai da aka tuntubi jami'an 'yan sanda na sashen rundunar "C", a ofishin rundunar da ke Asaba, jihar Delta, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar Delta, DSP Andrew Aniamaka da kuma kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mr. Muhammad Mustafa, sun tabbatar da faruwar wannan lamari.
Wani da ake kyautata zatoncewa mai kare hakkin dan Adam ne, sanye da kayan lauyoyi, ya shiga ofishin rundunar 'yan sanda na sashen "C", inda ya bukaci a sallami wasu mutane biyu da rundunar ta tsare bisa zarginsu da zama 'yan kungiyar asiri da har ta kaisu ga kashe wani.
Da isarsa, ya taras da babban jami'in da ke kula da sashen rundunar (DPO), CSP Aniete Uyo, inda a nan ne ya gabatarwa DPO da kansa, sai dai DPO ya kara bukatar neman wasu karin bayanai game da matsayin nasa, wanda hakan ya fusata shi mutumin.
KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa bamu kori jami'in da ya kashe diyar tsohon minista ba - Rundunar 'yan sanda
Ba tare da wata wata ba, wanda ake kyautata zamansa lauyan, ya kaiwa DPO naushi, inda ya mares hi tare da yaga masa kaya, daga bisani sai ya ci gaba da yin watsi da kayan ofishin.

Asali: Depositphotos
Jami'in kula da harkokin ta'addancin na ofishin sashen rundunar, DCO da kuma wani dan sanda, wadanda suka tsinke da wannan al'mari, ace wai har wani farar hula zai zo ya ci mutuncin shugabansu har a cikin ofishin rundunar. A kokarinsu na kai dauki, shi kansa DCO ya samu rauni a kansa, wanda kuma aka garzaya da shi asibiti don yi masa dinki.
Sai dai lauyan yayi kokarin tserewa, amma 'yan sanda da suka yi tsiri suka cimmasa tare da cafke shi, hadi da wasu mutane 3, yayin da sauran da ke tare da shi suka ranta a na kare.
La'akari da wannan rudani da ke tattare da wannan labarin, Kwamishin 'yan sanda, Mustafa, ya ce: "An samu damar cafke wanda ake kyautata zaton lauya ne tare da wasu mutane uku, wadanda suka aikata wannan aika-aikar. Zamu gufanar da su a gaban kotu; babu ta yadda zaka yi kutse a ofishin rundunar 'yan sanda kayi fada da jami'i kuma kasha lafiya."
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa, akwai wasu manyan mutane da suka sanya baki a cikin lamarin, inda suka tausasa zuciyar kwamishinan da ya ajiye maganar, ba sai anje gaban kotu ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng