Buhari ya kalubalanci yadda Obasanjo, Yar'adua da Jonathan suka gudanar da mulkinsu

Buhari ya kalubalanci yadda Obasanjo, Yar'adua da Jonathan suka gudanar da mulkinsu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kalubalantar tsoffin shuwagabannin kasar bisa gazawarsu na samar da abubuwan more rayuwa

- Buhari ya ce duba da irin makudan kudaden da kasar ta samu daga 1999 zuwa 2014, abun zai zama abun takaici ace kusan duk wasu kayan more rayuwa sun lalace a tsakanin shekarun

- Shugaban kasar ya kuma jinjinawa jakadan kasar ta Burtaniya, Arkwright, bisa dukkanin ayyukan da ya gudanar tsawon shekaru kusan uku da ya kwashe a kasar

A ranar litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kalubalantar tsoffin shuwagabannin kasar Nigeria bisa gazawarsu na saka jari mai tsoka a fanjin samar da abubuwan more rayuwa duk da irin tarin dukiyar da kasar ta samu karkashin shugabancin su.

A cewar wata sanarwa daga babban mai bashi shawara kan kafofin sada zumunta da watsa labarai, Mr. Femi Adesina, shugaban kasar ya yi wannan kalamin ne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Burtaniya a nan Nigeria wanda wa'adin aikinsa ya kare, Paul Arkwright, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya ce duba da irin makudan kudaden da kasar ta samu daga 1999 zuwa 2014, abun zai zama abun takaici da bacin rai ace kusan duk wasu kayan more rayuwa na kasar sun lalace a tsakanin shekarun.

KARANTA WANNAN: Ezekwesili: Hanyoyin da zanbi don samun nasara akan Buhari da Atiku a zaben 2019

Buhari ya kalubalanci yadda Obasanjo, Yar'adua da Jonathan suka gudanar da mulkinsu
Buhari ya kalubalanci yadda Obasanjo, Yar'adua da Jonathan suka gudanar da mulkinsu
Asali: UGC

Duk da cewa shugaban kasar bai ambaci sunan kowa ba, sai dai kowa ya san cewa tsoffinn shuwagabannin kasa, Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar'Adua da kuma Goodluck Jonathan su ne suka yi shugabanci daga 1999 zuwa 2014.

Sanarwar ta ruwaito Buhari yana cewa, "Mun mayar da hankali yanzu da samar da ababen more rayuwa, kamar su tituna, layin dogo, wutar lantarki da dai sauransu. Na so ace mun magance wadannan matsalolin a lokacin da kasar ke cike da kudi.

"Kudin da kasar ta samu daga 1999 zuwa 2014 a kididdige yake, amma babu wasu ayyukan raya kasa ko na azo a gani da akayi da kudin kan samar da ababen morewa rayuwa. Yanzu, muna iya bakin kokarinmu da 'yan kudin da muke samu. Kuma zamu ci gaba da kokartawa."

Shugaban kasar ya kuma jinjinawa jakadan kasar ta Burtaniya, Arkwright, bisa dukkanin ayyukan da ya gudanar tsawon shekaru kusan uku da ya kwashe a kasar, wanda ya bashi damar zagaya jihohi 30 cikin 36 da muke da su a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng