Akwai lauje cikin nadi game da kisan Janar Alkali - Majalisar malamai
Majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya watau Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta nuna shakkun ta akan tabbacin gano gawar Janar Alkali a cikin wani kabari da jami'an sojin Najeriya suka ce sun yi a ranar Juma'ar da ta gabata.
Majalisar dai ta malaman haka zalika ta kuma bukacin jami'an sojin da su bayar da gawar Marigayi Janar din ga iyalan sa domin a yi masa Sallah da sutura kamar dai yadda addinin muslunci ya tanada indai da gaske ne.

Asali: Twitter
Legit.ng Hausa ta samu cewa babban Sakatare Janar na majalisar koli ta malaman Ustaz Khalid Aliyu shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da lamarin.
A wani labarin kuma, Sanatan dake wakiltar mazabar jihar Yobe ta gabas a majalisar dattawa, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da da jam'iyyar sa ta APC da cewa kar su sa ma ran su samun kuri'in 'yan Arewa maso gabashin Najeriya a zaben 2019.
Sanatan ya bayyana cewa abu ne mai matukar wahala mutanen shiyyar su kara zabar shugaba Buhari domin basu ga wani canji ba takamaimai a rayuwar su tun bayar zabar tasa da suka yi a shekarar 2015.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng