Abin da ya sa aka budawa ‘Yan Shi’a wuta a Abuja – Inji Sojojin Najeriya

Abin da ya sa aka budawa ‘Yan Shi’a wuta a Abuja – Inji Sojojin Najeriya

- Mabiya Shi’a sun kai wa Dakarun Najeriya hari lokacin da ke muzahara

- ‘Yan Shi’an sun yi kokarin yin awon gaba da wata motar makaman Sojoji

- Hakan ta sa aka buda wuta har aka kashe wasu ‘Yan Shi’a har mutane 3

Abin da ya sa aka budawa ‘Yan Shi’a wuta a Abuja – Inji Sojojin Najeriya
An yi mummunan arangama tsakanin Mabiya Shi’a da Sojoji
Asali: Facebook

Mun samu labari cewa Dakarun Sojojin Najeriya sun ci karo da Mabiya addinin Shi’a a jiya da rana a Garin Zuba da ke cikin babban Birnin Tarayya a lokacin da su ke kokarin tafiya da wasu manyan makamai zuwa Garin Kaduna.

Sojojin kasar sun ci karo da ‘Yan Shi’a ne a daidai gadar Zuba inda su ka hana su wucewa. Bugu da kari kuma ‘Yan Shi’an sun kai wa Sojojin na Najeriya da duwatsu da kuma makamai masu illa inda su ka yi motocin Rundunar Sojin rotse.

KU KARANTA: Boko Haram su na neman Biliyan 100 kafin su saki yarinyar da su ka sace

‘Yan Shi’an sun ma yi kokarin yin awon gaba da manyan kayan yakin da Sojojin su ka dauko. Manjo James Myam shi ne babban Jami’in Sojojin kasar da ya bayyanawa manema labarai wannan a shafin Dakarun na shafin na Facebook.

Wannan ne dai ya sa Sojoji su ka buda wuta domin shawo kan lamarin inda hakan ya sa aka rasa mutane 3 daga cikin Tawagar ‘Yan Shi’an yayin da aka raunata wasu Sojojin Najeriya har 2 bayan an kai hari kan motocin Sojojin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng