Yadda yanar gizo ke taimakawa karuwan Najeria cin karen su ba babbaka
Tabbas daya daga cikin abubuwan da dan adam ya kirkiro da kuma yake taimakon sa a duniya gaba daya ita ce yanar gizo wadda kusan a iya cewa ta shiga rayuwar mutane ta kowane fanni musamman ma wajen saukaka rayuwa.
Haka zalika yayin da wasu ke anfani da yanar ta gizo a wajen saukaka ayyukan su na neman halaliyar su, wasu kuwa kan yi anfani da yanar ta gizo ne wajen aikata munanan laifuka a bangarori da dama na rayuwa.

Asali: Twitter
Legit.ng Hausa ta samu cewa a Najeriya ma dai kamar ko wace kasa a duniya, mutanen ta na matukar anfanuwa da yanar ta gizo - wasu a fannoni masu kyau da kuma anfani, wasu kuma a akasin haka.
Majiyar mu ta jaridar Punch tayi wani dan bincike akan yadda karuwai a Najeriya kan yi anfani da yanar gizon domin taimakawa wajen yin kazamar sana'ar su.
Karuwan a Najeriya yanzu sukan bude shafuka ne a dandalin sadarwar zamani daban daban inda sukan wallafa hotuna, bidiyo da kuma maganganun batsa da nufin jawo hankulan mabiyan su da kuma kwastomomin su.
Wasu daga cikin wadanda jaridar ta zanta da su sun bayyana cewa hakan ya fiye masu sauke da kuma tsaro fiye da tsayawar da sukan yi a bakin titi a da.
Su ma dai kwastomomin nasu da majiyar ta zanta da su, sun bayyana cewa wannan sabuwar hanyar ta fi sirri a gare su.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng