Kada ku kuskura ku zabi wanda ba shi da takardun kammala karatu - Sanusi ya gargadi 'yan Nigeria
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci 'yan Nigeria da su kauracewa zabar duk wani shugaba da ya gaza gabatar da takardun kammala karatunsa
- Sarki Sanusi ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta saka jarin tiriliyoyin nairorin da take batarwa a wajen tallafin man fetur zuwa fannin ilimantar da matasa a kasar
- Ya kuma zargi shuwagabannin Arewa na gazawa wajen samar da kyakkyawan muhallin koyo da koyarwa ga yara a makarantun Arewa
A ranar Asabar ne mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci 'yan Nigeria da su kauracewa zabar duk wani shugaba da ya gaza gabatar da takardun kammala karatunsa. Ya ce a lokutan baya 'yan Nigeria sun zabi shuwagabannin da basu da ilimi wanda kuma yasa ba sa baiwa ilimi muhimmanci idan sun shiga ofis.
Tsohon shugaban babban bankin Nigeria wanda ya yi jawabi a wani babban taron yaye daliban jami'ar Nile ta Nigeria da ya gudana a Abuja, inda kuma aka karrama sarkin da 'Honarary Degree' a fannin kimiyya, tare da shi akwai Sarki (Alaafin) jihar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III.
KARANTA WANNAN: Kashi na biyu: Nazari kan jihohin da jam'iyyar APC za ta iya rasawa a zaben 2019

Asali: Facebook
Ya ce: "Ya zamar mana wajibi mu kasance masu duba matakin ilimin shuwagabannin da zasu wakilcemu a matakan shugabanci daban-daban. Idan kuka yi duba ga kasar nan, mun zabi mutanen da basu da ilimi a matakan shugabanci daban-daban. Wannan ne kuma ba su dauki ilimi da daraja ba, saboda suma basu da ilimin.
"Muna bukatar mayar da hankali sosai akan wakilan da muke zaba zuwa majalisun dokoki dana tarayya, kuma mu tabbatar da cewa wadanda muka aminta dasu da yin dokoki a kasar, su kansu suna ilimi da kuma darajta ilimin kansa."
Sarki Sanusi ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta saka jarin tiriliyoyin nairorin da take batarwa a wajen tallafin man fetur zuwa fannin ilimantar da matasa a kasar. A cewarsa, kudaden da ake kashewa wajen gina hanyoyi, gadoji da titunan jiragen kasa, ya kamata a fara ilimantar da mata da kudin, yana nuni da cewa ilimi ne matakin bunkasa rayuwar kowacce al'umma.
KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: AFRICMIL ta maka Buhari kotu kan cire $496m don sayen jirgin Tucano
Sanusi ya ce: "Ya kamata mu koma saka jari a ilimi da kuma baiwa marasa galihu damar amfana da tiriliyoyin nairorin da ake kashewa wajen tallafin man fetur. Ya kamata wadannan kudaden a batar da su ne wajen ilimantar da matasa."
"Muna gina manyan tituna, amma mutanen da ke tafiya a kasa sunfi motocin da ke tafiya kan titin yawa, kuma mutanen nan mafi yawancinsu basu da ilimi ko taimako. Ilimi shine ginshikin komai na bunkasa rayuwar al'umma," a cewarsa.
Ya kuma zargi shuwagabannin Arewa na gazawa wajen samar da kyakkyawan muhallin koyo da koyarwa ga yara a makarantun Arewa.
Tun farko a jawabinsa, shugaban jami'ar, Farfesa Huseyin Sert, ya ce dalibai 21 ne suka kammala makarantar da matakin 'First Class' cikin dalibai 365 da jami'ar ta yaye.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng