Kashi na biyu: Nazari kan jihohin da jam'iyyar APC za ta iya rasawa a zaben 2019
Idan mai karatu bai manta ba, Legit.ng Hausa, ta fara wallafa wani nazari kan jihohi 9 da jam'iyyar APC za ta iya rasawa a zaben 2019, ta hanyar amfani da bayanan masu fashin baki kan harkokin siyasa a kasar. A kashin farko, mun kawo maku bayanai kan jihohi 4, a wannan kashin na 2, za mu karasa sauran jihohi 5 da suka rage cikon 9.
Jam'iyya mai mulki ra APC na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida, tare da yiyuwar rasa wasu manyan jihohi a zaben gwamnoni na 2019 da ke gabatowa, wanda hakan ba zai ma jam'iyyae sauki ba kamar yadda suka samu nasara a zaben 2015.
Ga dai bayanan jihohi 5 da suka rage cikon na 9, kamar yadda muka wallafa bayanan jihohi 4 a labarin baya.
KARANTA WANNAN: Nazari kan jihohin da jam'iyyar APC za ta iya rasawa a zaben 2019 - Kashi na daya

Asali: UGC
Rikici bai kare a jihar Benue ba
A jihar Benue, duknda cewar akwai kwantacciya da makirci da jam'iyyar ke fuskanta, har yanzu dai babu tabbas ko APC za ta iya shan kaye a zabe mai zuwa ganin cewa reshe na iya juyewa da mujiya a kowane lokaci.
Har yanzu dai APC da PDP ne suka mamaye jihar, sai dai sabbin jam'iyyu kamar su SDP, PRP da kuma APGA na zama barazana ga jam'iyyun biyu. Akwai rudani tsakanin jama'ar jihar na tunanin jam'iyyar danya kamata su zaba a 2019, sakamakon rikicin makiyaya da manoma da ya mamaye jihar, don haka ne ma masu fashin baki ke ganin cewa APC naniya rasa damarta a jihar.

Asali: Depositphotos
Hukuncin INEC zai mikawa jam'iyyar hamayya kujerar gwamnan Zamfara
Tun fara rikicin siyasar jam'iyyar daga 1999 lokacin tana APP, ta koma ANPP, har zuwa yanzu dabta koma APC, ta mulki Zamfara na tsawon shekaru 12, a mulkin Sanata Ahmad Sani Yarima da kuma Gwamna Abdul'aziz Yari.
Sai dai duk da sunan APC a Zamfara, jihar da jam'iyyun hamayya ba su da katabus. Idan har rikicin da ke faruwa yanzu a jam'iyyar yaki ci yaki cinyewa to kuwa za ta iya rasa jihar. INEC dai ta dage kan lallai APC ba zata gabatar da yan takararta a babban zaben 2019 ba, kasancewar ta gaza gudanar da zaben fitar da gwani kan lokaci. Idan kuwa wannan hukuncin ya tabbata, to cikim ruwan sanyi jam'iyyar hamayya za ta samu nasara a jihar Zamfara.

Asali: Depositphotos
Takun saka tsakanin Amaechi da Abe na yiwa APC barazana a jihar Rivers
Takun saka tsakanin ministan zirga zirga, Chibuike Amaechi da Sanata Magnus Abe na zama barazana ga nasarar APC a jihar Rivers. Masu fashin baki na ganin cewa a halin da APC ta ke ciki ba zata iya karawa da gwamnan jihar mai ci Nyesom Wike ba, wanda shima ke neman tazarce.
KARANTA WANNAN: KARIN BAYANI: Takai ya bayyana dalilan da suka tilasta masa fita daga PDP zuwa PRP
Amaechi na goyon bayan Arch. Tonye Cole dan takarar APC a jihar. Amma Abe na ganin cewa shine dan takarar APC a jihar karkashin tsagin jam'iyyar da ke bin kafar shugabanta Peter Odike.
Amma la'akari da hukuncin da kotu ta yanke a makon da ya gabata, APC ba ta da wata mafita, don kuwa tana iya rasa yan takara a zaben 2019.

Asali: Getty Images
Rashin sanin makoma na iya sa APC ta rasa jihar Imo
Jam'iyyar APC na ci gaba da fuskantar zaben 2019 a jihar Imo ba tare da sanin makoma ba, kasancewar har yanzu jam'iyyar ta kasa warware rikicin wanda zata baiwa tikitin takarar gwamnan jihar a zaben.
Tun a shekarar da ta gabata, lokacin da Gwamna Rochas Okorocha ya bayyana kudurinsa na baiwa surukinsa, Ugwumba Uche Nwosu, damar ya gaje shi, abubuwa da dama sun ci gaba da tabarbarewa a jam'iyyar. Kokarin wasu gungu a jam'iyyar na dakatar da shi ya kara rura wutar rikicin.
Haka zalika, yanzu rikici ne tsakanin Hope Uzodinma da Uche Nwosu.

Asali: Twitter
A Sokoto, Rarraba kuri'a zai shafi APC
A jihar Sokoto, akwai sauyin biyayya a tsakanin mambobin APC da ke bin tafiyar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, zuwa PDP. Da sauya shekar nan ta Tambuwal, an samu rabuwar kai a majalisar dokoki ta jihar, inda wasu suka koma PDP yayin da wasu suka ci gaba da zama a APC.
Wannan matakin ya kuma kulla takun saka tsakanin gwamnan da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakardan Wammako. Masu fashin baki na ganinncewa APC za ta samu babbar matsala a jihar ganin yadda za a karkasa kuri'un zabe a 2019, musamman yadda Tambuwal da Wammako ke ci gaba da sukar juna gabanin zaben.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng