KARIN BAYANI: Takai ya bayyana dalilan da suka tilasta masa fita daga PDP zuwa PRP
- Mallam Salihu Sagir Takai, ya fayyace gaskiya dalla-dallah, kan dalilan da suka tilasta mashi fita daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyyar PRP
- Takai ya ce sun cika duk wasu ka'idoji da dokokin shiga zaben fidda gwani na PDP amma daga baya jam'iyyar ta tauye mau hakki
- Ya ce sun rubuta takardar korafe korafe da kai kokensu amma itama uwar jam'iyyar ta gaza yi masu adalci a wannan halin da suka tsinci kansu a ciki
Tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi a jihar Kano, Mallam Salihu Sagir Takai, ya fayyace gaskiya dalla-dallah, kan dalilan da suka tilasta mashi fita daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyyar PRP mai alamar makulli.
A cewar tsohon dantakarar gwamnan jihar kano karkashin jam'iyyar PDP a zabe na 2019, wanda kuma jam'iyyar ta hana shi tikitin takara, Takai ya ce "Rashin adalcin da PDP ta yi mana a zaben fidda gwani abun Allah-wadai ne. Mun cika duk wasu ka'idoji da dokokin shiga zaben amma daga baya suka tauye mana hakki."
Takai ya ce a bisa doka, dole ne kowacce jam'iyya ta samar da dan takara awanni 48 kafin ta gudanar da zaben fitar da gwani, sannan kuma a bashi sunayen gaba daya wakilan da zasu kad'a kuri'a a zaben, amma a cewar Takai "babu ko daya da PDP ta yi, sai dai kawai muka ji labarin wai ta gudanar da zane fidda gwani a cikin gidan wani mutum."
KARANTA WANNAN: Ka tsaya matsayinka kada zancen duniya ya rude ka - Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu

Asali: UGC
Ya ce sun rubuta takardar korafe korafe inda suka bayyana kin amincewarsu da sahihancin zaben da aka ce an gudanar, tare da kai kokensu ga uwar jam'iyyar ta kasa, don a bi masu hakkinsu, sai dai a cewar sa "itama uwar jam'iyyar ta gaza yi mana adalci a wannan halin da muka tsinci kamu a ciki."
A cewar sa: "Wadannan dalilan ne ya sa na tilastawa kaina yanke shawarar barin PDP, daga bisani kuma, ni da magoya bayana, muka yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP, tare da fatan Allah ya bamu nasara a can," a cewar Mallam Salihu Takai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng