'Yan luwadi da madigo sun ce Atiku za su zaba a 2019 - sun bayar da kwararan dalilan su
Kungiyoyin 'yan luwadi, madigo da kuma 'yan daudu a Najeriya watau L8sbian, Gay, Bi3exual, and Transgender (LGBT) a turance sun bayyana matukar jin dadin su da jam'iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su na shugaban kasa a 2019.
Kungiyoyin dai sun kara da cewa su daman tuni sun yake hukuncin mara ma sa baya domin a cewar su, ba zai tauye masu 'yancin su ba na rayuwa kuma shi daman can baya da ra'ayin rikau irin na Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Rikicin jihar Kaduna ya sake rincabewa
Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban gamayyar kungiyoyin a yankin yammacin Afrika Msita Spinky Victor Lee ya bayyana hakan inda yace bayan sun yi duba na tsanaki akan dukkan 'yan takarar, sun yake hukuncin marawa Atiku baya.
A wani labarin kuma, Hukumar Hizbah dake da alhakin tabbatar da da'a a tsakanin al'umma ta jihar Kano dake a Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke wani kasurgumin kwarto da ya shahara wajen yin lalata da matan aure.
Daya daga cikin kwamandojin Hizbah din kuma mai magana da yawun ta, Ustaz Salisu rijiyar Lemo shine ya sanar wa da al'umma hakan a cikin wani dogon rubutu da yayi a shafin hukumar na dandalin sadarwar zamani.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng