Ganduje ya gayyacin limaman jihar Kano kan bidiyon da ke nuna shi yana karbar cin hanci
- Gwamnan jihar Kano ya gayyacin gaba daya limaman masallacin juma'a na jihar zuwa ga gidansa na kansa da ke titin Miyangu, a babban birnin jihar
- Ganduje ya kira wannan taron ne biyo bayan wata zazzafar huduba da Mallam Aminu Daurawa ya gabatar, dangane da bidiyon da aka hasko Ganduje yana karbar cin hancin $5m
- Ganduje bai ji dadin wannan huduba ta Daurawa ba. Don dakile sauran limamai daga bin sahun malamin,gwamnan ya kirasu tare da yi masu kashedi aka tsoma baki cikin harkokin siyasa
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a daren ranar Juma'a ya gayyacin gaba daya limaman masallacin juma'a na jihar zuwa ga gidansa na kansa da ke titin Miyangu, a babban birnin jihar.
Jaridar yanar gizo ta News Digest ta ruwaito cewa Ganduje ya kira wannan kwarya kwaryan taron ne biyo bayan wata zazzafar huduba da limamin masallacin juma'a na Ansarul Sunna, da ke Plaza Fagge, Mallam Aminu Daurawa ya gabatar, yana mai kira da ayi kwakkwaran bincike dangane da bidiyon da aka hasko Ganduje yana karbar cin hancin $5m.
KARANTA WANNAN: Yan Nigeria sun maidawa Buhari martani kan gazawarsa na gabatarwa INEC takardunsa
A hudubar da ya gabatar ta sallar Juma'a. Mr Daurawa ya ce mafi akasarin bidiyoyin da ake fitar da su a yanzu na zama hujjar da za a iya kafa bincike da ita, yana mai buga misali da wani lamari da ya afku a kasar Saudi, na kashe babban dan jarida Jamal Khashoggi.

Asali: Twitter
KARANTA WANNAN: Jonathan ya amince da shan kaye saboda durkushewar tattalin arziki - Fashola
"Hujjar da za a iya kafa da bidiyo, kamar misalin wacce aka yi amfani da ita wajen tabbatar da shigar Jamal Khashoggi cikin ginin jakadancin Saudiya a kasar Turkiya.
"Ya zama wajibi majalisar dokoki ta jihar Kano ta yi amfani da wannan bidiyo da ke nuna yadda gwamna ke karbar cin hanci don zama hujjar gudanar da kwakkwaran bincike don gano gaskiya da daukar mataki.
"Shekarau ya yi gwamna na tsawon shekaru 8. Kuma ya taba rike mukamin minista. An tuhume shi kuma an gurfanar da shi gaban kotu. Don haka babu wani aibu don an gudanar da bincike tare da tuhuma kan bidiyon karbar cin hancin," a cewar Mr Daurawa.
KARANTA WANNAN: Faransa za ta fara koyar da darasin 'Larabci' a makarantun gwamnatin kasar
Sai dai a hannu daya, wannan hudubar ta Daurawa ta harzuka gwamnan jihar ta Kano, inda har yakan ya tilastashi kiran limaman masallatan Juma'a na jihar don gargadarsu akan tsoma baki cikin harkokin siyasa.
"Ganduje bai ji dadin wannan huduba ta Daurawa ba. Don dakile sauran limamai daga bin sahun malamin,gwamnan ya kirasu tare da yi masu kashedi aka tsoma baki cikin harkokin siyasa." a cewar wata majiya da ta halarci taron, wanda kuma ta bukaci a sakaya sunanta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng