Abun da za muyi wa Nnamdi Kanu idan ya kuskura ya shigo Najeriya - Rundunar sojin Najeriya

Abun da za muyi wa Nnamdi Kanu idan ya kuskura ya shigo Najeriya - Rundunar sojin Najeriya

- Sojin Najeriya sun fadi abun da za suyi wa Nnamdi Kanu idan ya shigo Najeriya

- Sun ce za su natsar da shi da ma dukkan wani hatsabibi

- Yanzu dai Nnamdi Kanu na kasar Isra'ila

Hedikwatar hukumar jami'an rundunar sojojin Najeriya watau Defence Headquarters (DHQ) a turance dake a garin Abuja, babban birnin tarayya ta fada da kakkausar murya abinda zata yi wa hatsabibi Nnamdi Kanu idan har ya kuskura ya shigo kasar nan.

Abun da za muyi wa Nnamdi Kanu idan ya kuskura ya shigo Najeriya - Rundunar sojin Najeriya
Abun da za muyi wa Nnamdi Kanu idan ya kuskura ya shigo Najeriya - Rundunar sojin Najeriya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan sanda sun cafke wanda ya hau dogon karfe saboda Atiku

Wannan dai kamar yadda muka samu, ya biyo bayan wata barazanar da shi Nnamdi Kanu din dake zaman shugaban haramtattar kungiyar nan ta 'yan Aware dake neman a raba Najeriya watau Indigenous People of Biafra (IPOB) na cewa zai hargitsa kasar idan yazo.

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai da yake yiwa 'yan jarida jawabi hedikwatar ta tsaro, Birgediya Janar John Agim ya bayyana cewa tuni hukumar ta kafa wata runduna ta musamman wadda ta sanya wa suna '777' da nufin koyawa dukkan wani hatsabibi hankali.

A kwanan baya-baya din nan dai maganar ta Nnamdi Kanu ta kara tashi biyo bayan hotunan sa da suka bulla a kasar Isra'ila tun bayan da ya tsere ya bar kasar ta Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng