Akwai barazanar yunwa a Jigawa sakamakon hare-haren da kwari ke kaiwa gonakin shinkafa
Manoman shinkafa a karamar hukumar Auyo da ke jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnati da ta yi gaggawan daukar mataki akan kwarin dake lalata gonakin shinkafa a yankin.
Shugaban kungiyar manoman shinkafa, Malam Mohammed Garba ya yi wannan kira a lokacin da daraktan kasar, Sasakawa Global 2000 (SG 2000), Prof. Sani Ahmed-Miko ya ziyarci kungiyar Auyo a ranar Juma’a, 26 ga watan Oktoba.

Asali: Depositphotos
Yace kwarin da tsuntsayen na zuwa ne daa yankin Baturiya a Guri inda suka lalata gonakin shinkafa da yawa a yankin.
KU KARANTA KUMA: Jaridar tattalin arziki ta duniya ta yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019
Ya ce akwai bukatar gwamnatin jihad a ta tarayya su dauki matakin gaggawa duba ga tarin gudunmawarsu wajen samar da shinkafa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng